• 18 Jun, 2025

Jami'ar Calabar Ta Dakatar Da Wani Malami Bisa Laifin Magudin Jarabawa

Jami'ar Calabar Ta Dakatar Da Wani Malami Bisa Laifin Magudin Jarabawa

1000000885.jpg

Shugabar jami'ar Calabar Farfesa Florence Obi, ta ce sun dakatar da Malamin jami'ar Joseph Akpan bisa laifin magudin jarabawa.

Ana zargin Akpan wanda shi ne shugaban tsangayar koyon hada magunguna da magudin jarabawa inda ya tauye hakkin dalibai a kalla 235 a cikin 242.

Shugaban jami'ar ta kara da cewa dalibai biyar ne kacal suka tsira da ha'incin malamin.

Farfesa Florence Obi ta ce malamin.ya canja sakamakon jarabawar daliban inda ya bawa wasu guda biya maki ba tare da sun rubuta jarabawar ba.

Akpan dai ya amsa laifin sa yayinda majalisar koli ta jami'ar ta Calabar ta gayyace shi domin bincike.

Da yake amsa laifin sa, malamin ya yi ikrarin kara wa da bada kyaitar maki ga daliban ne domin daga kimar tsangayar.

Duk da haka, majalisar kolin jami'ar bata gamsu ba inda ta dauki matakin dakatar da shi tare da kwace kujerar shugaban tsangayar.

Tun ba yau ba ne ake samun malaman jami'ar a Najeriya da hannu a magudin jarabawa ko lalata da yanmata.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.