• 18 Jun, 2025

Jami'ar Azman Ta Fidda Jerin Kwasa-kwasan Ta

Jami'ar Azman Ta Fidda Jerin Kwasa-kwasan Ta

Jami'ar Azman Ta Fidda Jerin Kwasa-kwasan Ta

screenshot-20240724-111632-1721816299639.jpg

Jami'ar Azman dake Kano ta fitar da jerin kwasa-kwasan ta domin masu sha'awar yin karatu a jami'ar.

Jami'ar ta sanar da fara siyar da takardun nuna sha'awar shiga jami'ar a kafafen yada labarai da ma shafukan ta na yanar gizo.

Jami'ar ta bayyana kwasa-kwasan zamani da matasa zasu iya karanta don dogaro da kansu bayan sun kammala karatun.

Kwasa-kwasan sun hada da Computer Science, da Biotechnology da Data Science da Software Engineering.

Akwai kuma kwasa-kwasai kamar Health Science da Public Health da Hospital Management da Health Information Management.

Sauran kwasa-kwasan sun hada da Cybersecurity da Information Technology da Aviation Management da Procurement Management da ma sauran dunbun kwasa-kwasai masu tafiya da zamani duk a jami'ar ta Azman dake birnin Kano, arewa maso yammacin Najeriya.
 

Jami'ar Azman dai jami'a ce mai zakan kanta wato Private University. An gina ta ne domin bunkasa harkar ilimi a jihar Kano da ma arewacin Najeriya baki daya.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.