
Gwamnatin Najeriya ta bawa kamfanin gine-gine na Julius Berger kwanaki 7 ta karbi kudi Naira biliyan 740.7 domin fara aikin titin Abuja zuwa Kaduna da Zaria zuwa Kano, ko ta rasa kwangilar baki daya.
Ministan ayyuka David Nweze Umahi ne ya furta haka a jiya Laraba yayin wani taro da shugabannin kamfanin a Abuja.
Mai magana da yawun ministan Orji Uchenna Orji ne ya bayyana matsayin ministan akan kwangilar gina titin.
Ministan ya nuna bacin ransa kan tsadar aiki da kamfanin na Julius Berger ke yi, inda kamfanin baya duba halin matsin tattalin arziki da Najeriya ke fama dashi.
David Umahi ya ce kamfanin ya dade yana amfana da gwamnatin kasar a fannin samun kwangiloli amma baya duba hakan.
Ministan ya ce ya zama dole kamfanin ta yanke hukuncin amincewa ko akasain haka cikin mako guda.
Minista Umahi ya kara da cewa gwamnati ba za ta lamunci karin kudi kan kwangilar ba ko da kobo ne, domin da farko kudin kwangilar Naira biliyan 710 ne amma saboda bata lokaci yanzu kudin ya karu da Naira biliyan 30.
David Umahi ya ce, watanni 14 kenan da yarjejeniyar kwangilar amma kamfanin na wasa da hankalin gwamnati.
Umahi ya ce, wannan ne damar karshe da gwamnati ke bawa kamfanin. Idan ta yi kunnen uwar shegu, za a karbi kwangilar a bawa wani kamfani.