• 18 Jun, 2025

ICPC Ta Cafke MaI Kula Da Kudade Na Hukumar Hajji Kan Zargin Halin Bera

ICPC Ta Cafke MaI Kula Da Kudade Na Hukumar Hajji Kan Zargin Halin Bera

8gegza4t-400x400.jpg

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ICPC ta cafke babban daraktan Hukumar kula da jin dadin alhazan kasar bisa zargin rub-da-cika da kudi kimanin Naira biliyan 90.

Kudin dai na daga cikin kudaden da gwamnatin tarayya ke bawa Hukumar don tallafa mata wajen gudanar da ayyukan ta.

Hukumar ta ICPC ta yi awun gaba da darakta mai kula da harkokin kudi na hukumar Hajjin ta kasa yayin samamen da ta kai shelkwatar Hukumar Hajjin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka daraktan Hukumar Hajjin na hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawar domin amsa tambayoyi da ma sauran bincike.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.