
Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya yi wata ganawa da kwamitin zaman lafiya kan zabukan da ke tafe a jihohin Ondo da Edo da ke kudu maso yammaci da kudu maso kidancin kasar.
Mahmood Yakubu ya jagoranci manyan ma'aikatan hukumar zaben mai zaman kanta da suka hada da kwamishinonin hukumar da daractoci da ma masu bawa hukumar sjawara kan tsare-tsaren zabuka.
Shugabannin hukumar zaben sun shirya ganawar ne domin tattauna wa kan muhimmancin zaman lafiya gabanin zabukan gwamna da hukumar za ta gudanar a ranar 21 ga watan Satumban wannan shekarar.
An yi ganawar ne a babban sakatariyar kwamitin zaman lafiya ta kasa baki daya da ke birnin tarayya Abuja.