• 18 Jun, 2025

Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Cafke Soyinka

Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Cafke Soyinka

dss1-768x511-1.jpg

Jami'an hukumar tsaron sirri ta DSS ta kama wani dan jarida mai suna Adejuwon Soyinka.

An kama dan jaridan wanda editan shiyya ne na jaridar Conversation Africa a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke birnin Eko.

Soyinka ya shiga hannun jami'an DSS ne bayan ya dawo dage wata balaguro kasar Ingila.

Rahotanni sun tabbatar da cewa anyi awun gaba da shi kuma aka kashe wayoyin sa domin hana shi magana.

Yanzu haka dai Soyinka yana tsare a magarkamar hukumar tsaron ta farin kaya batare da cikakken bayani kan halin da yake ciki ba.

Adejuwon Soyinka ya sauka daga jirgin kamfanin Virgin Atlantic ne misalin karfe 5:40 na safiyar yau Lahadi inda nan take jami'an na DSS sukayi mishi diran mikiya.

Kawo yanzu dai babu wani dalili da  jami'an tsaron sirrin suka fitar game da makasudin kama dan jaridan.

Mai magana da yawun hukumar tsaron ta DSS Peter Afunanya ya ce hukumar  batada masaniya game da kama wani dan jarida.

Ba yau jami'an tsaro a Najeriya ke cin zarafin 'yan jarida ba a kokarin su na dakile 'yancin fadin albarkacin bakin da dokar kasa da ma ta duniya ta bada.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.