
Masu ruwa da tsaki a harkar ilimi a Najeriya sun fidda 140 a matsayin mafi kankancin maki don samun rurbin shiga jami'a a kasar.
Hukumomin sun ce, maki 100 kuma ita ce mafi kankanci kafin mutum ya samu gurbin shiga kwalejin kimiyya da fasaha da ma kwalejin ilimi.
Hukumomin sun dauki matsayar ce bayan ganawa ta shekarar 2024 kan shirye-shiryen fara bada gurabun karatu a makarantun gaba da sakandare a kasar a birnin tarayya Abuja.
Shugaban hukumar shirya jarabawar JAMB Farfesa Ishaq Oloyede ya ce, maki 140 ta samun gurbin karatun jami'a da maki 100 ta shiga kwalejin kasar su ne mafi kankanci da ake bukata.
Farfesa Oloyede ya ce, duk da maki 140 da mak 100 da aka amince da su, kowace jami'a tana da ikon amfani da nata maki sama da 140 da 100 amma ba kasa da haka ba.