
Hukumar shirya jarabawar JAMB ta ce, akwai wasu manyan makarantun kasar dake bawa yara 'yan shekaru 10 gurbin karatu a Najeriya.
Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede ya ce, akwai wasu jami'o'i a kasar da ke karya dokar bada gurbin karatu a manyan makarantun kasar.
Oloyede ya ambaci jami'ar tarayya ta birnin Eko da jami'ar tarayya ta Obafemi Awolowo dake Ille-Ife a cikin jami'o'in kasar da ke karya dokar bada gurbin karatu.
Ya ce, suna bawa 'yan shekaru 10 gurbin karatu a jami'o'in saboda son zuciya. Oloyede ya nuna rashin jin dadin sa kan lamarin.
Oloyede ya bada misalin wata 'yar Najeriya da ta nemi gurbin karatun digiri ta biyu a kasar Jamus inda aka gano ta kammala karatun digirin farko a Najeriya tana da shekaru 15.
Farfesa Ishaq Oloyede ya ce, jami'ar ta kasar Jamus tayi mamaki matuka, inda ta tuntube su domin tabbatar da hakikanin gaskiya.
Oloyede ya ce, hakan na nuna cewa, ko a kasashen turai babban kuskure ne a bawa dan shekara 10 gurbin karatu a jami'a domin bai mallaki hankalin kanshi ba.