
Hukumar shirya jarabawar JAMB ta ce ta fara tantance cibiyoyin rijista da ma rubuta jarabawar ta sbekar 2025 mai zuwa.
Hukumar ta ce tantance cibiyoyin matakin farko ne na shirye-shiryen gudanarda jarabawar ta JAMB shekara mai zuwa.
A wata sanarwa da ta fitar ta hannun mai magana da yawunta Dakta Fabian Benjamin, hukumar ta JAMB ta ce duk wata cibiyar hada-hadar na'urar kwamputa za ta iya ziyartar shafinta na yanar zigo, wato https://www.jamb.gov.ng/Pdfs/CBT_centre_requirements.pdf.
Benjamin ya ja hankalin cibiyoyin da su sanarda hukumar a rubuce idan suna bukatar a tafi da su a jarabawar ta 2025.
Fabian Benjamin ya ce, masu sha'awar shiga harkar jarawabar za su tuntubi babban rigistran hukumar ta JAMB ta hannun Daraktan shiyya ko na jiha a jihohinsu.
Benjamin ya ce Daraktan shiyya ko na jiha ne zai duba yiwuwar tantance cibiyoyin domin amincewa da su ko akasin haka.
Benjamin ya bayyana cewa cibiyoyin da su ka cancanta ne kadai za su samu bayanai dangane da ranar tantancewar, wanda za a fara a wata mai kamawa.