• 18 Jun, 2025

Hukumar Kwallon Kafa A Najeriya Tana Neman Sabon Koci

Hukumar Kwallon Kafa A Najeriya Tana Neman Sabon Koci

Hukumar Kwallon Kafa A Najeriya Tana Neman Sabon Koci

fb-img-17222914546662438.jpg

Hukumar kwallon kafa a Najeriya ta NFF tayi shelar neman mai cike gurbin kocin kungiyar kwallon kafa ta Flying  Eagle.

Hukumar tace duk mai sha'awar jagorancin kungiyar kwallon kafar kuma mai abubuwan da ake bukata, zai iya neman wannan aikin.

Hukumar mai kula da kwallon kafar ta kasa na neman kocin da zai jagorancin yan tamolan masu kasa da shekaru 20 wadda aka fi sani da Under-20 a turance.

Hukumar ne ta sanar da hakan a shafukan ta na yanar gizo inda ta bayyana cewa ta na bukatar wanda ke da lasisi na "CAF B" da  gogewa a jagorancin kungiyar kwallon kafa na a kalla shekaru biyar.

Akwai kuma bukatar duk wanda zai cike gurbin jagotancin kungiyar kwallon kafar na da kwarewa kan tsarin wasan kwallon kafa ta Najeriya da ma gogewa wajen iya shugabancin da hulda da jama'a.

Hukumar ta kwallon kafar tace za ta rufe karban neman aikin kocin ranar 4 ga watan Agusta mai kamawa.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.