• 18 Jun, 2025

Hukumar Aikin Yan Sanda Ta Fidda Ranar Fara Horas Da Sabbin Dauka

Hukumar Aikin Yan Sanda Ta Fidda Ranar Fara Horas Da Sabbin Dauka

screenshot-20240809-132134-1723206140322-1723206164968.jpg

Hukumar kula da aikin yan sandan Najeriya ta umarci wadanda suka yi nasara su kama hanyar su ta zuwa guraren horaswa daban-daban da ke fadin kasar domin karbar horo.

Hukumar ta bayyana cewa za ta fara horas da wadanda aka dauka aikin yan sandan ne gobe Asabar 10 ga watan Agusta wannan shekarar.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar Ikechukwu Ani ne ya sanar da haka a wata takarda da sanyawa hannu.

Mista Ani ya ce wadanda su ka ga sunayen su ne kadai za su halarci guraren horaswan da aka shirya a fadin kasar.

Ikechukwu Ani ya kara da cewa huraswan zai dauki kwanaki goma ne, wato daga ranar 10 ga wannan watan (gobe) zuwa ranar 20.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.