• 18 Jun, 2025

Haryanzu Ana Ci Gaba Da Kai Ruwa Rana Tsakanin Gwamna Fubara Da Wike A Jihar Rivers

Haryanzu Ana Ci Gaba Da Kai Ruwa Rana Tsakanin Gwamna Fubara Da Wike A Jihar Rivers

1000001279.jpg

Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya ce haryanzu kotun daukaka kara bata maida wasu yan majalisar dokokin jihar kujerun su ba.

Yan majalisan dai magoya bayan tsohon gwamnan jihar ne Nyesom Wike wadanda suka yi ta kai ruwa rana da gwamna Fubara mai ci.

Kotun daukaka karar ta tarayya ta kori yan majalisan ne bayan ta same su da laifin sauya sheka daga jami'yyar PDP zuwa jam'iyyar APC.

Yanzu haka dai kotun ta dakatar da aiwatar da kasafin kudin jihar Rivers na shekarar 2024 wanda ya kai Naira biliyan 800 sakamakon rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.

Yan majalisan guda hudu wadanda Edison Ehie ke jagoranta kuma magoya bayan gwamna Siminalayi Fubara ne suka rantaba hannu a kasafin kudin cikin awa 24.

Sakamakon haka ne kotun ta tarayya ta dakatar da gwamna Siminalayi Fubara daga ikon aiwatar da kasafin kudin.

Abin jira a gani dai shi ne ranar da rikicin siyasar tsakanin gwana Fubara da Wike zai kawo karshe.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.