
Wasu daga cikin wdanda suka tsira daga iftila'in ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri sun bayyana cewa ambaliyar ita ce mafi muni a cikin shekaru 30 da suka gabata.
Wadanda suka tsira sun mika godiyar su ga Allah da ya kara musu numfashi ya tsirar da su daga iftila'in ambaliyar.
Rahotanni sun nuna cewa har yanzu Jami'an bada agajin gaggawa na NEMA da sojoji da ma Gwamnan jihar Borno na ta aikin kokarin ceto mutane daga ambaliyar ruwan.
Wani mai suna Goni Ba Usman wanda aka hango yana zaune a gindin bishiya yana kuka ya bayyana cewa har yanzu bai sa na mujiya ga matar sa da 'ya'yan sa 5 ba sakamakon ambaliyar.
Ya ce tun ranar Talata bai ga iyalen nasa ba. Goni ya ce babu abinda zai ce sai dai mika lamarin ga Ubangiji domin shi ne mai rayawa kuma shi ne mai kashewa.