
Kamfanin mai na NNPCL ya ce haryanzu ba a samu karin gawa daga hadarin jirgin sama da ya afku ba, duk da kokarin da mahukunta ke yi.
Kamfanin man na kasa ya bayyana cewa bayan wadanda aka samu guda uku, kawo yanzu babu wani karin gawa da aka gano sakamakon mummunan hadarin.
Idan ba a manta ba dai wani jirgin sama mai saukar ungulu na kanfanin jiragen saman Eastwind Aviation, ya fadi da mutane 8 ranar alhamis da ta gabata a filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Fatakwal.
Saukar gaggawar ta yi sanadin hadari inda aka samu rasa rayukan mutane uku. Tun rananr ne hukumomi masu ruwa da tsaki a harkar hadarin jirgin sama ke faman gano ragowar mamatan, amma haryanzu babu labari.
Kamfanin man na NNPCL ta bakin daraktan sa Mele Kyari, ya kara da cewa, mahukuntan sun tabbatarda cewa za su ci gaba da neman mamatan har sai inda karfinsu ya kare.
Gwawwakin mutum uku ne kadai daga cikin mutane 8 da ke cikin jirgin aka samu tun bayan da jirgin mai saukar ungulu ya yi hadari.
Kamfanin ya ce suna cikin jimamin rashin abokan aikinsu, kuma suna kara jajantawa iyalen wadanda suka rasa rayukansu a hadari, inda su ke musu addu'o'i.