• 17 Jun, 2025

Har Yanzu Akwai Ministocin Da Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Kore Su—Cewar Tsohon Dan Majalisar Wakilan Najeriya

Har Yanzu Akwai Ministocin Da Ya Kamata Shugaba  Tinubu Ya Kore Su—Cewar Tsohon Dan Majalisar Wakilan Najeriya

1000009434.jpg

Tsohon dan majalisar wakilan Najeriya kuma Shugaban marasa rinjayi a wancan lokacin Wunmi Bewaji ya shawarci shugaba Bola Tinubu ya duba yiwuwar korar wasu karin ministocinsa.

Wunmi Bewaji ya ce akwai wasu da dama a cikin ministocin Shugaba Tinubu da ya kamata a koresu domin basusan ayyukansu ba.

Wunmi ya shawarci shugaba Bola Tinuba ya yi hakan ne bayan shugaban ya kori ministoci 10 a watan da ya gabataa.

Yayinda ya ke ganawa da gidan jaridar Tribune, Tsohon dan majalisar ya ce har yanzu akwai tarkace da ke amsa sunayen ministoci amma ba su yi komai a ofisoshinsu ba.

A daya bangaren, wunmi ya ce ita kanta gwamnatin na Bola Tinubu ta gaza ta hanyoyi da dama musamman bangaren kudin shigar kasar.

Wunmi ya ce, gwamnati da ta gabata na Goodluck Ebele Jonathan ta yi almabazzaranci da dukiyar kasa, domin lokacin ya kamata Najeriya ta yi abin kanta, saboda man fetur na da daraja a kasuwannin duniya, amma ba a yi hakan ba.

Dan majalisar Wunmi ya kara da cewa, lokacin da Buhari ya zama Shugaban kasa ma babu wani sauyi da kasar ta samu cikin shekaru 8 da ya yi a karagar mulki, sai dai koma baya.

Wunmi ya ce abubuwan da Goodluck da Buhari  su ka yi su ne su ka jefa kasar a cikin halin da ta ke ciki a yanzu.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.