
Hamshakin attajirin nan Femi Otedola ya bawa jami'ar Augustine da ke Legas gudumawar kudi Naira biliyan 3.7 domin bunkasa tsangayar koyarda ilimim kere-kere.
Otedola mai mukamin cansilo a jami'ar ya furta hakan ne yayin bikin bada takardun kammala karatu karo na 6 a jami'ar.
Femi Otedola ya bayyana burinsa na ganin jami'ar ta zama kan gaba a Najeriya a fannin bada ilimin kere-kere a fadin kasar.
Tun ba yau ba ne dai hamshakin attajirin ke bada gudumawa a fannoni daban-daban a Najeriya musamman a kudancin kasar domin cigaban al-umma.
A baya ma Otedola ya bawa jami'ar gudumawar kudi Naira biliyan 2 domin gina tsangayar tun daga farkonta a shekarar 2023.
Femi Otedola ya kuma rabawa dalibai 750 kudi Naira miliyan 1 kowannensu a baya domin su biya kudin makaranta bayan jami'ar ta nada shi a matsayin cansilo.
Otedola ya yi kira ga daliban jami'ar da su dukufa akan karatu ta hanyar sa neman ilimi a zukatarsu domin cigaba.