• 17 Jun, 2025

Hafsan Sojojin Najeriya Lagbaja Ya Rasu

Hafsan Sojojin Najeriya Lagbaja Ya Rasu

1000008522.jpg

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanarda rasuwar Babban hafsan sojan kasa na Najeriya Janar Taoreed Lagbaja.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ne ya fitar ta cewa Janar Lagbaja ya rasu a jiya Talata da dare bayan shafe wani lokaci yana jinya.

Shugaba kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga yan'uwa da abokan arziki da ma rundunar sojin Najeriya baki daya bisa rashin da aka yi.

Janar Lagbaja ya mutu yana da shekaru 56 a duniya bayan a baya an garzaya da shi asibitin kasar waje, yayinda daga bisani aka dowo da shi gida Najeriya.

A baya dai yan Najeriya sun yi ta cece-kuce kan matsayin lafiyar Janar Lagbaja, inda suka nuna kokwanto kan sahihin bayani akan shi.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.