• 17 Jun, 2025

Gwamnonin Arewa Sunyi Fatali Da Kudurin Shugaba Tinubu Kan Karin Harajin VAT

Gwamnonin Arewa Sunyi Fatali Da Kudurin Shugaba Tinubu Kan Karin Harajin VAT

1000006891.jpg

Wata sabuwar rigima ta barke game da kudurin harajin VAT da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike majalisar dokokin kasar, yayin da kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta fito fili ta yi fatali da kudurin, musamman kan yadda za a fasalta rabon harajin.

A farkon watan Oktoban wannan shekarar ne Shugaba Tinubu ya aike da wasu kudurori hudu kan tsare-tsaren kudi ciki har da kudurin harajin VAT gaban majalisar dokokin Najeriya domin neman amincewarta.

Haraji VAT wasu kudade ne da ake dora wa kan wasu kayayyaki ko abubuwa da aka sarrafa idan mutum ya saya daga kamfanoni.

Wani masanin tattalin arziki a Najeriya  ce a yanzu haka a Najeriya ana biyan kashi 7.5 na kudin abin da mutum ya saya.

Abin da ke faruwa shi ne ko me ka saya, ana lissafa maka karin kashi 7.5 cikin 100 na adadin kudin da ka saye shi domin ka biya.

Ana karbar  harajin ne a kamfanin da ke sayar da kaya ko samar da ayyukan, sannan ya mika shi ga asusun ofishin hukumar karbar haraji ta kasa.

Kamar yadda yake kunshe cikin kudirin karin harajin VAT na 2024, ba kowane abu ne ake dora wa harajin ba domin akwai wasu abubuwan da ba a biya musu harajin VAT.

Daga cikin abubuwan da aka kebe akwai kayan abinci kamar hatsi, da madara, da burodi, da ruwan sha, da abubuwan da suka shafi ilimi.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.