• 18 Jun, 2025

Gwamnatin Tinubu Ta Hana 'Yan Kasa Da Shekaru 18 Shiga Jami'a

Gwamnatin Tinubu Ta Hana 'Yan Kasa Da Shekaru 18 Shiga Jami'a

Gwamnatin Tinubu Ta Hana 'Yan Kasa Da Shekaru 18 Shiga Jami'a

fb-img-17213054665721062.jpg

Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta hana bawa masu kasa da shekaru 18 guraben karatu a makarantun gaba da sakandare.

Ministan ilimin kasar Farfesa Tahir Mamman ne ya furta haka a yau Alhamis, yayin wata ganawa da hukumar shirya jarabawar JAMB a Abuja.

Ministan ya umarci jami'o'in Najeriya su janye bawa masu kasa da shekaru 18 guraben karatu.

Tahir Mamman ya ce, dokar shekaru 18 na cikin tsarin karatu na 6-3-3-4 a kasar, don haka, ba sabon abu be ne.

Ministan ya ce, akwai wani shiri daga gwamnatin tarayya na horas da 'yan Firamare ilimin dogaro da kai musamman wadanda ba su samu guraben karatun jami'ar ba.

Dokar da haramta bawa 'yan kasa da shekaru 18 guraben karatu, ta shafi jami'o'in kasar da kwalejin kimiya da fasaha da ma kwalejin ilimi.