
Shugaban kamfanin kera motoci a Najeriya
Innoson Chukwuma ya ce kamfanin sa ya shirya domin samar da motoci masu amfani da iskar gas a kasar.
Shugaban ya ce, motocin za su taimaka wajen saukaka wahalan da talakawan Najeriya ke ciki ta fannin sufuri duba da tsadar man petur da yan kasar ke fama da ita.
Mista Chukwuma ya bayyana haka ne bayan ya gana da shugaba Bola Tinubu a kokarin gwamnatin kasar na kawo sauki wa yan kasa a fannin sufuri.
Chukuma ya ce yan Najeriya za su yi murmushi idan kamfanin sa ya kera motocin aka fara amfani da su a fadin kasar.
Ya ce, tuni kamfanin sa ya yi nisa wajen kera irin wadannan motocin, inda ya ce gwamnatin tarayya za ta hada gwiwa domin cimma wannan kudirin.