
Gwamnatin jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya ta musanta karban motar kayan abinci 20 da gwamnatin tarayya tayi ikrarin turawa jihar.
Gwamnatin Adamawan ta furta haka ne a daidai lokacin da gwamnatin Bola Tinubu tace ta tura buhunan kayan abin mota 20 zuwa kowace jiha a fadin kasar.
Gwamnatin jihar Adamawa ta bakin wani kwamishinan jihar tace, tana iya kokarin ta don ganin ta saukakawa yan jihar wahalhalun da suke ciki, amma dai ba ta karbi kayan abinci ba ko buhu guda daga gwamnatin tarayya.
Gwamnatin jihar har walau ta ja hankalin yan Adamawa da su guji duk abinda zai kawo tashin hankali a jihar da ma Najeriya baki daya.
Gwamnatin jihar Adamawan tace zaman lafiya abu ne mai muhimmanci ga rayuwar al'umma da ma ci gaban jihar mai albarka.
Tace, akwai bukatar yan Adamawa suyi taka-tsan-tsan da taza zaune tsaye duba da illolin da zanga-zangar EndSARS ta haddasa a baya a jihar Lagas.