
Gwamnatin Najeriya ta ciyo bashin Dala biliyan 6.45 daga bankin duniya cikin watanni 16 kacal da Shugaba Tinubu ya hau karagar mulki.
A kwanan nan ne dai gwamnatin ta karbo bashin Dala biliyan 1.57 daga bankin duniya domin gudanar da ayyukan bunkasa kasa inda ake sa ran adadin bashin zai iya karuwa cikin watanni masu zuwa.
A yanzu haka dai jimillan bashin da kasar ta ciyo cikin shekaru biyar ya kai Dalar Amurka biliyan 24.088.
Masana a kasar na tofa albarkacin bakin su game da hadarin ciyo bashi daga bankin duniya da sunan ayyukan bunkasa kasa ba tare da lissafi ba.
Wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke ikrarin yi da basukan sun hada da bunkasa wutar lantarki wanda zai lashe kudi Dala miliyan 750, da gina mata wanda zai ci kudi Dala miliyan 500.
Taimakawa ilimin 'ya'ya mata shi ma na daga ciki inda zai lashe zunzurutun kudi Dala miliyan 700, da ma sauran ayyuka da gwamnatin ta ambata.
Da yawan 'yan Najeriya basa farin ciki da dabi'ar gwamnatin kasar na ciyo bashi barkatai duba da lalacewar abubuwan more rayuwa kamar su tituna da ruwan sha da sauran su da gwamnati ta gaza inganta su duk da basukan da ta ke ciyowa.
Haryanzu dai babu kwakkwarar dalilai na ciyo basuka da gwamnatin Najeriya ke yi shekara-da-sekaru domin 'yan kasar basa ganin ayyuka masu ma'ana da gwamnati ke yi da su.