• 18 Jun, 2025

Gwamnatin Shugaba Tinubu Ba Za Ta Janye Salon Mulkin Ta Ba —Cewar Jam'iyyar APC

Gwamnatin Shugaba Tinubu Ba Za Ta Janye Salon Mulkin Ta Ba —Cewar Jam'iyyar APC

1000001322.jpg

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shaida wa yan adawa cewa su daina tunanin gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta sauya matsayinta dangane da matakan da take dauka a kasar.

Jam'iyyar ta kuma yi watsi da ikirarin yan adawa na yin magudin zaben gwamna a jihar Edo da aka gudanar ranar 21 ga watan da ya gabata.

A ranar Alhamis din nan ne, Kwamitin Amintattu na Jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi APC da magudi a zaben da aka gudanar a jihar, inda PDP ta ce jami'iyyar mai mulki ta tafka magudi ne domin cimma wata manufa ta mayar da Najeriya kan tsarin jam'iyya guda daya tilo.

A yayin gabatar da jawabi ga manema labarai a birnin Abuja, shugaban jam'iyyar PDP ya bayyana damuwarsa kan halin da Najeriya ke ciki na tabarbarewar tattalin arziki wanda ya ce salon mulkin APC ne suka haddasa.

A nasu bangaren, mai magana da yawun jami'iyyar APC Alhaji Bala Ibrahim ya bayyana cewa, jam'iyyar APC na cike da kyawawan manufofi don ci gaban Najeriya.

Yan Najeriya dai na ci gaba da kokawa kan matakan gwamnatin shugaba Tinubu da suka jefa su cikin kuncin rayuwa, inda a baya-bayan nan kasa da wata daya aka kara samun tashin farashin litar man fetur har sau biyu a daidai lokacin da takawa ke kokowa kan tsadar rayuwa.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.