
Gwamnatin Najeriya ta ce tana shirin raba wa talakawan kasar miliyan 20 tallafin kudi domin rage musu radadin rayuwa.
Ministan kudi da tattalin arziki na Najeriya, Wale Edun ne ya bayyana haka a lokacin babban taron tattalin arzikin kasar karo na 30 a Abuja.
Minista Edun ya ce gwamnatin za ta yi amfani da ribar da ta samu a watanni shidan farkon shekarar 2024 wajen raba tallafin don inganta rayuwar talakawan kasar da ke fama da matsin tattalin arziki.
A jawabinsa na bikin zagayowar ranar yancin kai na 1 ga watan Okotoba, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin kasar ta samu ribar naira tiriliyan 9.1 a watanni shidan farkon shekarar da muke ciki.
Adadin ya ninka abin da aka samu a shekarar da ta gabata, inda aka samu naira tiriliyan 4.06 a daidai irin wannan lokacin.
Ministan kudin kasar ya ce shirin zai shafi kashi 60 cikin 100 na talakawan Najeriya.
Minista Edun ya kuma jaddada kudurin gwamnatin kasar na mayar da hankali wajen inganta harkokin noma da masana'antu da albarkatun man fetur da gidaje, wadanda ya ce su ne manyan bangarorin tattalin arzikin kasar.