
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amincewa matatar man Aliko Dangote samar da man jirgin sama
Gwamnatin ta bakin ministan sufurin jiragen saman kasar Festus Keyamo ta ce, matatar man Dangote ce kadai za ta rika samar da man jirgin daga yanzu.
Ministan ya kara da cewa gwamnati ta kammala duk wani shirin tabbatar da hakan.
Festus Keyamo ya kara da cewa amfani da Naira wajen saya da sayar da man fetur zai kara wa Naira daraja a harkokin kasuwancin duniya.