
Hukumar bada ilimi a matakin farko wato UBE a jihar Kwara ta ce za ta dauki sabbin ma'aikata 1,611 a fadin jihar.
Shugaban hukumar Farfesa Shehu Adaramaja ne ya sanar da haka a babban birnin jihar Illorin.
Shehu Adaramaja ya ce za su dauki masu gigiri guda 695 da masu NCE 605 da masu gadi 200 da sauran ma'aikata 111 domin bunkasa harkar ilimin Firamare a jihar.
Adaramaja ya kara da cewa ma'aikatan da za a dauka za a raba su ne cikin kananan hukumomi 16 daidai da adadin bukatar kowace karamar hukuma.
Shehu ya ce daukan ma'aikatan ya biyo bayan amincewar gwamnan jihar ne Abdulrahman Abdulrazaq sakamakon guraben wasu da sukayi ritaya daga aiki.
Adaramaja ya ce za a maida hankali ne wajen kwarewa da girmama shaidar karatu yayin daukar ma'aikatan.