• 18 Jun, 2025

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kama Dan Jarida Kan Zargin Bata Suna

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kama Dan Jarida Kan Zargin Bata Suna

zmjnzaey-400x400.jpg

Gwamnatin jihar Kano ta kama tare da  tasa keyar wani dan jarida zuwa gida kaso sakamakon zargin batanci da ya yi wa gwamnatin jihar.

Dan jaridan mai suna Muktar Dahiru da ke aiki da gidan radiyon tarayya Pyramid FM ya yi rubutun bata suna ne a shafukan sada zumunta kan Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ana kuma zargin Muktar Dahiru da yi wa Sarki mai martaba Muhammad Sanusi Lamido Sanusi batanci a cikin rubutun nasa.

Muktar Dahiru, a cikin ruburun nasa ya bata wa wasu jami'an gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

An cafke dan jaridan ne tun ranar Alhamis kuma yanzu haka ya na gidan maza biyo bayan abinda ya yi.

Muktar Dahiru dai ya sha tura abubawa kamar interview da ya yi da 'yan jam'iyyar adawa ta APC a jihar a shafukan sa na sada zumunta, wadanda su ke zargin Gwamna Yusuf da cinhanci da rashawa.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.