
Gwamnatin jihar Enugu ta rushe maboyar masu garkuwa da mutane a bayan gari a birnin Enugu da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Gwamnatin jihar ta ce masu garkuwan na amfani da wasu gidaje wajen ajiye wadanda suka yi garkuwa da su.
Gidajen da aka rushe sun hada da wani gida da ba a kammala ba da ke da wata hanya ta karkashin kasa a Nkwubor Layout inda aka samu makamai da albarusai da dama.
Akwai kuma wani gidan gona da ake noman kayan marmari da kiwon kaji da kananan dabbobi a garin Ogbeke Nike cikin karamar hukumar Enugu ta gabas a jihar.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Peter Mbah a wata sako ya ce an samu bindigar AK-47 da bindigogin pump action guda bakwai da ma wani nau'in bindigan guda biyu.