• 17 Jun, 2025

Gwamnatin Bola Tinubu Ta Kashe Naira Biliya 20 Don Gyaran Gidaje Biyu Na Mataimakin Shugaban Kasa Da Ke Abuja Da Legas Yayinda Talakawan Kasar Ke Fama Da Yunwa

Gwamnatin Bola Tinubu Ta Kashe Naira Biliya 20 Don Gyaran Gidaje Biyu Na Mataimakin Shugaban Kasa Da Ke Abuja Da Legas Yayinda Talakawan Kasar Ke Fama Da Yunwa

1000009191.jpg


Gwamnatin Najeriya karkashin mulkin shugaba Bola Tinubu ta kashe kudi har Naira biliyan 5 wajen gyaran gidan mataimakin shugaban kasa da ke birnin Legas.

Wani bayanai da ke shafin GovSpend da ke tatso bayanan gwamnatin kasa ya wallafa rahoton yadda gwamnati ke kashe kudin.

Bayanin ya nuna cewa gwamnatin kasar ta kashe wani bangare daga cikin kudin wajen bawa kamfanin gine-gine mai suna Denderi Investment domin yin kwangilar gyaran.

Gwamnatin ta kuma kashe wasu kudaden ranar 5 ga watan satumban wannan shekarar ta ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila domin gyaran gidan.

Hukumar babbar birnin tarayya Abuja ta ce ita ma za ta kashe zunzurutun kudi Naira biliyan 15 domin gina wani kawataccen gida na mataimakin shugaban kasar.

Abin tambaya dai shi ne yadda gwamnatin kasar ke kashe makudan kudade akan gidajen biyu na mataimakin shugaban kasa, inda a cikin guda zai zauna, yayinda 'yan kasar ke fama da talauci da yunwa.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.