
Rigima tsakanin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da mai gidansa Rabiu Musa Kwankwaso ta yi tsamari, inda rahotanni ke nuna cewa gwamnan ba ya daga wayar Kwankwaso yanzu haka.
Bayanai sun nuna cewa gwamna Abba ya ki ya hadu da Kwankwaso domin wata ganawa na gano bakin zaren matsalolin da suka addabi jam'iyyar mai mulki a jihar Kano, sa'annan yanzu kuma baya amsa kirar wayar Kwankwaso.
Rigimar dai ta fara ne tun watan Maris na wannan shekarar, inda ake zargin jagora Rabiu Musa Kwankwaso da nada dukkan shugabanni kananan hukumomin 44 na riko, ba tare da bawa gwamna Abba Kabir Yusuf damar kawo ko da mutum guda ba.
Rigima ta biyu kuma ta fara ne lokacin da wasu 'ya'yan jam'iyyar suka shawarci gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsaya da kafarsa, wanda hakan ke nufin ya ci gashin kansa ya jefar da Kwankwaso.
A yanzu haka dai wasu daga jam'iyyar ta NNPP sun samu izini daga kotu domin karbar shugabancin NNPP daga hannun Kwankwaso, yayinda wasu a Abuja ke kokarin neman samun damar yin sheka zuwa jam'iyya APC.
Wasu daga cikin masu neman raba kan jam'iyyar ta NNPP su ne Baffa Bichi da Mohammed Diggol, wadanda aka dakatar da su daga kujerunsu na Sakatare da Kwamishinan jihar sakamakon furuchin nuna kiyayya ga Rabiu Musa Kwankwaso.
Sauran 'yan siyasar da ke hura wutar rikicin sun hada da dan majalisar dattawa Kawu Sumaila da dan majalisar wakilai Daga mazabar Dala, Aliyu Sani Madakin-Gini.
Yanzu dai rahotanni sun nuna cewa tuni gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauki shawarar tsayawa da kafarsa domin samun 'yancin kansa a matsayinsa na gwamna mai cikakken iko.
Wani rahoto ya nuna cewa, tun ba yau ba gwamna Abba Kabir Yusuf ke muradin korar wasu kwamishinonin jihar saboda rashin kwarewarsu, amma sakamakon ladabi da ya ke wa Rabiu Musa Kwankwaso,hakan bai yiwuba.
Yanzu dai gwamna Abba Kabir Yusuf ya gaji kuma ya kosa, don haka, rahotanni su nuna ya fara juyawa jagorar jam'iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso baya.
Abin jira a gani dai shi ne yadda za ta kaya tsakanin bangarorin biyu da ke hararar juna cikin jam'iyyar adawar mai mulkin jihar Kano.