• 17 Jun, 2025

Gwamnan Jihar Taraba Agbu Kefas Ya Gana Da Kamfanin Gine-Gine Na Kasar Chana Domin Fara Ayyukan Cigaba A Jihar Sa

Gwamnan Jihar Taraba Agbu Kefas Ya Gana Da Kamfanin Gine-Gine Na Kasar Chana Domin Fara Ayyukan Cigaba A Jihar Sa

1000007856.jpg

Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas ya gana da shugaban kamfanin gine-gine na kasar Chana a birnin tarayya Abuja.

An gudanarda ganawar ne a gidan tsohon janar din sojan Najeriya T Y Danjuma da ke Asokoro a Abujan?

Gwamnan ya yi ganawar ne tareda wasu jami'an gwamnatin jihar ta Taraba wadanda suka hada da mataimakin gwamna Aminu Alkali da yan majalisar dokokin jihar da sauran kusoshin gwamnati.

Taron dai da gwamnan ya shirya na da zummar fara aiwatarda tsarin cigaba na shekara 2024 a jihar ta hanyar gine-ginen tituna da rukunan gidaje a jihar tareda hadin gwiwar kamfanin na kasar kasar Chana.

Da ya ke bayani, gwamna Agbu Kefas ya nuna farin cikinsa da shirin hadin gwiwar, inda ya ce, hakan zai bashi damar cimma muradunsa na ayyukan da ya sa a gaba a jihar.

Gwamna Agbu Kefas ya bayyana cewa ganawar zai maida hankali kan abubuwa guda uku na cigaba wadanda suka hada da wutar lantarki da tattalin arziki da ayyukan gina birane da kauyuka.

Gwamna Agbu Kefas ya ce nan ba da dadewa ba jihar Taraba za ta zama kan gaba wajen samarda wutar lantarki a fadin Najeriya.

A nasa bangaren, kwararren injiniyan gine-gine Alex Oniegbu ya ce, kundin tsarin cigaban jihar ta Taraba zai shafi kowace karamar hukuma a jihar ba babban birnin jihar Jalingo ba ce kadai.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.