
Gwamnan jihar Katsina Umaru Dikko Radda ya ce, a shirye yake ya aiwatar da hukuncin kotun koli na bawa kananan hukumomi 'yancin su.
Gwamnan ya furta haka ne ta bakin mai magana da yawun sa Ibrahim Kaula Mohammed a birnin Katsina.
Gwamnan ya ce, tuni kananan hukumomi na cin gashin kansu zuwa wani mataki a jihar ta Katsina.
Umaru Radda ya ce, Jihar Katsina jiha ce mai biyayya da hukuncin kotu, don haka, za ta yi aiki karkashin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Gwamnan ya bayyana cewa, gwamnatin sa na aiki kafada-da-kafada da kwamishinan Shari'ar jihar don ganin samun nasarar bawa kananan hukumomi 'yancin su.