
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya taya Daniel Bwala murnar samun mukamin mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkar yada labarai.
A wata takarda da mai magana da yawun Gwamna Zulum ya fitar, gwamnan ya ce, Daniel Bwala mutum ne da ya kware kan harkar Shari'a da ma harkar hulda da jama'a baki daya.
Zulum ya bayyana cewa ya na da kwarin gwiwa akan Bwala sakamakon gogewa da ya yi wajen tafiyarda harkar labaru musamman wajen kare mutuncin shugaban kasa a wannan lokaci.
A matsayinshi na dan jihar Borno, Gwamna Zulum ya ce Bwala zai bada gudumawarsa a mulkin shugaba Bola Tinubu ta hanyar kare manufofin shugaban kasa.
Gwamna Zulum ya yi wa Daniel Bwala fatan alheri a sabon ofishinsa na mai bawa shugaban kasa shawara kar yada labarai.