• 17 Jun, 2025

Gwamnan Borno Zulum Ya Marabci Tsohon Shugaban Kasa Buhari A Maiduguri

Gwamnan Borno Zulum Ya Marabci Tsohon Shugaban Kasa Buhari A Maiduguri

1000008400.jpg

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya marabci tsohon shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari a ziyararsa da ya kai Maiduguri.

Muhammadu Buhari ya kai ziyarar bazata a babban birnin jihar ta Borno domin jajantawa jama'an jihar kan iftila'in ambaliyar ruwa da ta kassara gidaje da dukiyoyin mutane a birnin Maiduguri a watan Satumban da ya gabata.

Tsohon Shugaban kasan ya tafi kasar waje lokacinda ambaliyar ruwan ta afkawa Maiduguri, inda ya tura wakilansa zuwa jihar da gudumawar kudi Naira miliyan 20.

Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yayinda ya samu labarin ambaliyar ta afku, ya girgiza mutuka domin a matsayinsa na tsohon gwamnan jihar na  mulkin soja, ya tabbata ambaliyar za ta yi mummunar ta'adi.

Gwamna Babagana Zulum da ma Shehun Borno Abubakar Umar Garbai Elkanemi sun nuna farincikinsu da ziyarar ta Muhammadu Buhari.

Buhari ya je Maiduguri ne tare da tsohon sakataren gwamnatin kasa Boss Mustapha da Sulaiman Adamu da Sanata Hadi Sirika da Tsohon Minista Isa Ali Pantami da Garba Shehu da sauransu.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.