• 18 Jun, 2025

Gwamnan Borno Na Kan Gaba A Kokarin Ceto Al-ummar Maiduguri Daga Ambaliyar Ruwa

Gwamnan Borno Na Kan Gaba A Kokarin Ceto Al-ummar Maiduguri Daga Ambaliyar Ruwa

fb-img-17260883240147726.jpg

An hango gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum cikin ruwan da ambaliyar Dam din Alau ta haddasa a birnin Maiduguri.

Tunda iftila'in ambaliyar ta faru gwamnan Zulum na tare da al-umma a Maiduguri babu dare babu rana domin duba halin da su ke ciki.

Gwamnan a cikin hotuna na aiki ne da Jami'an tsaron sojoji don ganin an ceto wasu daga cikin wadanda ambaliyar ya yiwa tarko a gidajen su.

Kawo yanzu dai dubannin mutane ne aka ceto daga ambaliyar da ta kassara gidajen su da dukiyoyin su.

Gwamntin jihar Borno karkashin jagorancin Gwamnan Zulum na iya kokarin ta domin kai wa mutane dauki sakamakon ambaliyar da irin ta ta faru shekaru 30 da suka gabata

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.