
Gwamnan Jihar Bayelsa Sanata Douye Diri ya ja hankalin sabbin sakatarorin din-din-din na jihar da su gudanarda ayyukansu bisa gaskiya da adalci a dukkan ma'aikatun jihar.
Douye Diri ya furta haka ne jiya Talata yayinda ya ke rantsarda sabbin sakatarorin 15 a dakin taro da ke gidan gwamnatin jihar a birnin Yenagoa.
Gwamna Diri ya taya sabbin sakatarorin murnar samun kujerun, inda ya jinjina musa kan kokarin kaiwa matsayin a aikin gwamnati.
Douye Diri ya ce, akwai bukatar sakatarorin su yi aiki bisa bin ka'idojin aiki, inda ya ce, hakan ne kadai zai mutunta su a cikin al-umma.
Gwamna Diri ya ce, ya na da kwarin gwiwa kan sabbin sakatarorin wajen gudanarda ayyukansu cikin kwarewa ta hanyar yin aiki da kananan ma'aikata.
Gwamna Diri ya ce, shi da mataimakinsa sun fuskanci matsin lamba ciki da wajen jihar ta Bayelsa yayinda su ke zaban sakatarorin, amma duk da haka, ba su damuba, saboda sun bi ka'idojin nada sakatarorin.