
Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya ce tsare-tsaren gwamnatin shugaba Bola Tinubu marasa kan gado ne suka jefa yan kasar cikin masifar yunwa da bacin rai.
Gwamna Mohammed ya ce hakan ne ya haddasa zanga-zanga a fadin Najeriya da gwamnatin kasar ta kasa gano bakin zaren ta.
Bala Mohammed ya furta haka ne yayin kaddanar da yakin neman zaben kananan hukumomin jihar da za'a gudanar ranar 17 ga wannan watan.
Gwamna Mohammed ya ce akwai bukatar shugaban kasa Bola Tinubu ya yi amfani da ilimin da Allah ya bashi domin yin watsi da duk wani shiri da bazai taimaki talakawan Najeriya ba.
Bala Mohammed ya ce ya zama dole shugaba Tinubu wanda shi ke da wuka da nama ya sake tunani matukar yana son kawo karshen zanga-zanga.