
Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed ya ce daga yau ya rushe ma'aikatar kula da kananan hukumomi da masarautun jihar.
Bala Mohammed ya furta hakan ne a gidan gwamnati a birnin Bauchi yayin rantsar da sabbin kwamishinoni da mai bashi shawara na musamman kan harkokin tsaro.
Gwamnan ya dauki matakin ne domin tabbatar da cikakken 'yancin kananan hukumomin jihar kamar yadda kotun koli ta bada umarni watannin baya da suka gabata.
Bala Muhammed ya bayyana cewa zai bawa kananan hukumomin jihar Bauchi damar cin gashin kan su domin al-ummar kananan hukumomi da karkara su amfana.
Gwamnan ya ce kananan hukumomin za su fara juya kudaden su batare da wani sa ido ko tsangwama ba.