• 17 Jun, 2025

Gwamna Maimala Buni Na Jihar Yobe Ya Ce Ba Za Ta Yiwu Ba Bindiga A Ruwa

Gwamna Maimala Buni Na Jihar Yobe Ya Ce Ba Za Ta Yiwu Ba Bindiga A Ruwa

1000006545.jpg

Gwamnan jihar Yobe, Maimala Buni, ya ce suna daukar matakan gaggawa na magance matsalolin da suka addabi arewa da suka hada da matsalar wutar lantarki da kuma matsalar tsaro da ta addabi yankin.

Maimala Buni ya ce suna aiki da kwarraru domin magance matsalar wutar lantarki da ta addabi yankin.

Gwamnan a zantawarsa da manema labarai ya bayyana cewa akwai maganar amfani da hasken rana da wasu dabaru da za a iya mafani da su wadanda za su kawo karshen matsalar ta wuta a arewa.

Gwamnan ya ce ba za su sauke wa gwamnatin tarayya nauyin da ke kanta ba saboda akwai hakkokin arewa a kan ta, don haka ya zama dole su hada duka domin su inganta wutar lantarki.

Maimala Buni ya musanta zargi da wasu ke yi na cewa babu hadin kai tsakanin gwamnaonin arewacin Najeriya, inda ya ce babu gaskiya a zargin.

Maimala Buni ya ce, akwai hadin kai sai dai kawai maganar da suka yi ita ce ta yin abu bai daya, tunda matsalolin duk iri daya ne.

Gwamnan ya ce abunda za su yi wanda zai zaburar da arewa, musaman kan tatalin arzki da tsaro da ilimi da noma a  dukkan jihohin arewa musamman arewa maso gabas da arewa maso yamma, ind amatsalolin tsaro suka yi tsamari su ne abubuwanda suka tattauna.

Gwamnan ya ce hadin kai ne ya sanya suke da shugaba wanda shi ne gwamnan Gombe Inuwa Yahya.

Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun ce sun dauki matakan bai-daya na magance matsalolin da suka addabi yankin.

Gwamnonin sun ce sun cimma matsaya a taron da suka gudanar a Kaduna, kan yadda za su tunkari matsalolin tsaro da tattalin arziki da suka addabi yankin da matsalar wutar lantarki da ake fuskanta da kuma daukar matakan magance su.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.