• 18 Jun, 2025

Gobara Ta Kama Kasuwar Wayar Salula A Lokoja

Gobara Ta Kama Kasuwar Wayar Salula A Lokoja

screenshot-20240913-111651-1726222636872.jpg


Anyi asarar dukiya na miliyoyin Naira sakamakon gobara da ta tashi a kasuwar wayoyin salula a birnin Lokoja da ke jihar Kogi.

Wutar gobarar ta fara ne da safiyar jiya Alhamis wandda sakamakon wutar lantarki mai karfi ne ta haddasa gobarar.

Daya daga cikin masu sayar da wayoyin salular Muhammed Yahaya wanda ya rasa dukiyar sa ya ce tabbas wutar lantarki mai karfi da aka kawo ciki dare ne makasudin gobarar.

Yahaya ya kara da cewa akwai gidaje da ke makwabtaka da kasuwan da suka yi asara, domin kayayyakin wutan lantarkin gidajen sun kone sakamakon gobarar.

Muhammed Yahaya ya mika rokon 'yan kasuwan ga gwamnati jihar Kogi domin neman taimakon kudi da ma sake gina kasuwar.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.