
Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi shugaban Rasha Vladimir Putin ya kiyayi ruruta wutar yakin kasar Ukraine.
Donald Trump ya furta haka ne a wayarsa ta farko tun zama shugaban Amurka, inda ya tattauna da Shugaban na Rasha Putin kan yakin kasar Ukraine.
Shugaba Trump ya tunatarda Vladimir Putin cewa, ya sani kasar Amurka na da karfin soja a nahiyar turai domin tunkarar kowace irin matsala.
Haryanzu dai akwai kallon hadarin kaka tsakanin Trump da Putin, wanda za a iya cewa na kasa na dabo tun shekarar 2016, lokacin da Trump ke yakin neman zaben shugabancin Amurkan.
A baya Donald Trump ya yaba namijin kokari da Vladimir Putin ya yi na yakar kasar Ukraine, amma yanzu da alamar ya sauya tunani kan yakar kasar ta Ukraine.
Ba da dadewa ba ne dai Shugaban na Rasha Vladimir Putin da Donald Trump su ka yi wata ganawa kan cimma zaman lafiya a nahiyar Turai baki daya, ta hanyar warware rikicin.
Akwai wani batun da ke nuna shugaban Amurkan Donald Trump ka iya kyale kasar ta Rasha ta mallakin wasu yankunan kasar Ukraine a lokacin da ya ke zantawa ta wayar salula da Vladimir Putin na Rasha.
Abin jira a gani dai shi ne yadda za a kawo karshen rigimar yakin tsakanin Rasha da Ukraine da yadda wasu kasashen nahiyar Turan kamar Amurka ke shiga tsakanin lamarin.