
Shahararren marubucin adabin nan asalin dan Najeriya wato Farfesa Wole Soyinka ya ce, tsohon shugaban kasar Amurka kuma dan takarar shugaban kasar a yanzu, Donald Trump babban makaryaci ne na gaske.
Wole Sonyinka ya furta hakan ne a shirye-shiryen sa na bikin cika shekaru 90 a duniya. Soyinka ya bayyana Donald Trump a matsayin annoba kuma babban barazana ga duniya.
Soyinka ya ce, Donald Trump Dan shekara 78 ya tsallake rijiya da baya a yakin neman zabe a Pennsyania, inda wani yayi kokarin hallaka shi. Duk da haka, Donald Trump ya ce yana cikin koshin lafiya, dan rauni kadai ya samu a gefen kunnen sa na dama.
Soyinka ya ce, Najeriya ta na da wani makaryaci, amma bai shahara kamar Donald Trump ba. Duniya bata taba yin makaryaci irin Donald Trump ba. Wole Sonyinka ya ce, Donald Trump ya raina hankalin Amurkawa ta hanyar sharara musu karya.