• 18 Jun, 2025

Dole Ne Mu Zakulo 'Yan Shian Da Suka Kashe Jami'an Mu—Cewar Babban Sufeton 'Yansandan Najeriya

Dole Ne Mu Zakulo 'Yan Shian Da Suka Kashe Jami'an Mu—Cewar Babban Sufeton 'Yansandan Najeriya

police-confirm-arrest-of-97-shiites-720x536.jpg

Babban sufeton 'yansandan Najeriya Kayode Egbetoku ya umarci rundunar 'yansandan kasar su farauci 'yan kungiyar Shia da suka kashe 'yansanda biyu sa'annan suka raunata wasu da dama a Abuja.

Yayin da yayi Allah wadai da lamarin, babban sufeton 'yansandan ya ce ya zama dole a zakulo makasan domin hukunta su.

Ya ce rundunar ba za ta lamunci kisan jami'an ta a bakin aiki ba domin hakan babban barazana ne a harkar tsaro.

Mai magana da yawun rundunar 'yansandan Najeriya ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce kawo yanzu sun cafke mutum 97 tare da gano makamai.

Adejobi ya ce ba za su lamunci faruwar hakan nan gaba ba. Ya kara da cewa dole ne su dauki matakin dakatar da haka.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.