
Naira ta samu daraja da bai taka kara ya karya ba a kasuwar saye da sayarda kudade a jiya Alhamis.
Nairar ta samu tagomashi daga 1,740 a kan kowace Dalar Amurka guda zuwa 1,730 jiya Alhamis a kasuwannin canjin kudade a kasar.
Nairar har wa yau ta fadi warwas a kasuwar canjin kudade ta duniya, inda ta tsinci kanta a matsayin 1,650.2 akan kowace Dalar Amurka.
Bayanai sun nuna cewa darajar Nairar a kasuwannin duniya ta fadi ne daga 1,645.4 zuwa 1,650.2 a ranar Laraba.
Yawan Dalar Amurka da aka saba harka da ita a kasuwa ta ragu da 9.33 cikin 100, inda Dala miliyan 236.84 da aka saba kaiwa kasuwa ta ragu zuwa Dala miliyan 214.73.