
Kudin Najeriya ta kara daraja a kasuwannin saye da sayarwar kudaden kasashen duniya a Najeriya.
Darajar Nairar ta tashi daga 1,730 a kan kowace Dalar Amurka zuwa 1,725, inda Naira ta samu tagomashin Naira 5 na daraja a ranar Laraba a kasuwar canjin kudade.
Jim kadan daga baya, Nairar ta samu nakasu, inda ta fadi kasa warwas da tazarar Naira 44 da kobo 32 duka a ranar ta Laraba.
Yayinda Naira ke fuskantar rugujewar daraja a kasuwannin canjin kudaden duniya, ita kuma Dalar Amurka na ta hauhawa wajen daraja.
Kudin Najeriya dai na cigaba da fuskantar barazanar koma baya a yan shekarun nan tun lokacin shugabancin tsohon gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele.
A kwanan nan ne bankin duniya ta ayyana kudin Najeriya cikin jerin kudaden da ke kan gaba wajen rashin daraja a yankin Afrika da ke kudu-da-hamada.
Abin jira a gani dai shi ne dawowar jarajar Naira a kasa da ma duniya baki daya ko akasin haka, yayinda Naira ta zama kamar mushen gizaka ciki da wajen Najeriya.