• 18 Jun, 2025

Dan'sanda Ya Kashe Mahaifin Sa

Dan'sanda Ya Kashe Mahaifin Sa

Dan'sanda Ya Kashe Mahaifin Sa

nigerian-police-logo-1-1.png

Wani dan sanda ya kashe mahaifin sa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a bayan ofishin rundunar 'yan sandan jihar Borno dake unguwar Modugannari a Maiduguri.

Dan sandan mai sunan Wadzani yana aiki ne a karkashin majalisar dokokin jihar ta Borno.

Mahaifin Wadzani shima Dan sanda ne da yayi ritaya a matsayin ASP.

Yanzu haka dai an cafke tare da tsare Wadzani a ofishin 'yansanda dake unguwar GRA a birnin Maiduguri domin gudanar da bincike.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.