
Attajirin dan kasuwan Najeriya Aliko Dangote ya tallatawa kamfanin NNPCL katafaren matatan mai da ya gina a birnin Eko.
Siyar da matatan na da nasaba da abinda Dangoten ya kira matsin lamba da hasada da wasu ke yi da matatan ciki da wajen Najeriya don ganin sun hana matatar tasiri.
Dangote ya yanke hukuncin yada kwallon mangoro ya hutawa da kuda don mahasada su zuba ruwa a kasa su sha.
Dangote ya ce, yanada yakinin idan ya siyar da matatar man zai samu kwanciyar hankali, tunda ba'a son shi da harkar a Najeriya.
Dangote ya ce, nan ba da jimawa ba, zai cika shekaru 70 a duniya, don haka babu dalilin da zai sa ya damu kanshi domin abinda yake da shi ya isa ya karasa sauran rayuwar sa.
Ali Dangote ya ce, duk kokarin sa na gina matatar man yayi ne don kasar sa Najeriya ta ci gaba. Amma tunda wasu ba sa so, babu wata matsala.