
Matatar man Dangote ta fara gwajin tace man petur inda ake sa rai za ta tsunduma aikin tace man yadda ya kamata a tsakiyar wata mai kamawa na Satumba.
Matatar man na Aliko Dangode na da karfin tace mai har lita dubu dari shida da hamsin a kowace rana da zaran ta fara aiki yadda ya kamata.
Aliko Dangote wanda ya kashe makudan kudi har dalar Amurka biliyan ashirin domin gina katafaren matatar mana a yanzu man diesel da wasu mayuka kadai yake samarwa a matatar.
A baya dai matatar man ta Dangote tayi yunkurin fara samar da man petur a watan Mayun wannan shekarar amma hakan bai yiwu ba. Matatar tayi wani yunkurin a watan Yuli duka hakan bai yiwu ba.
Ana sa ran duk lokacin da matatar man Dangote ta fara cikakken aiki, za ta kawo karshen jigilar fitar da danyen mai zuwa kasashen turai domin tacewa da ma rage shigo da man daga kasashen ketare.
A farkon watan Agustan nan ne dai gwamnatin Najeriya ta nada wani kwamiti don tilasta sayarwa matatar man Dangote da sauran matatun mai na cikin gida danyen mai domin tacewa a gida daga wata mai kamawa na Satumba.
Fadar gwamnatin Najeriya ta bada umarnin yin hakan ne domin inganta matatun man cikin gida da niyyar kawo canji a harkar albarkatun mai a kasar.
An dauki matakin ne yayin wata ganawa da jami'an gwamnatin kasar masu ruwa da tsaki kan harkar mai suka gunadar a birnin tarayyar kasar Abuja inda daga bisani ministan kudi ya sanar da matakin na gwamnati.