
Rahotanni sun tabbatar da cewa man petur daga matatar man Dangote ba zai zama mai araha kamar yadda 'yan Najeriya ke fata ba.
Rahotannin sun nuna cewa matatar man zai sayar da litar har Naira 1000 idan Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantaba masa hannu a kan hakan.
Wani da ke kusa da fadar shugaban kasar Najeriya shi ne ya bankado kokarin na matatar man Dangote.
Ministan albarkatun man petur Heineken Lokpobiri ya sha alwashin man petur zai wadata a fadin kasar bayan ganawa da yayi da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima kan batun.
Idan da gaske matatar man Dangote na jiran farashin litar mai daga fadar shugaban kasa, lalle tsugune ba ta kare ba ga dan Najeriya, domin matatar man Dangote ba za ta kawo wani canji da 'yan kasa ke sa rai ba.
Har yanzu dai 'yan Najeriya na ci gaba da shan wahala kan dogayen layuka a gidajen mai a biranen kasar sakamakon rashin man petur da ma tsadar sa.