
Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyya mai mulki ta APC Gbenga Hashim ya shawarci shugaba Bola Tinubu da ya warware matsalolin da za su jefa kasar cikin zanga-zanga.
Hashim yace abu ne mai sauki idan shugaban kasa ya saurari bukatun yan kasa da zummar warware su domin kaucewa shiga zanga-zangar da za'a fara ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa.
Hashim yace haka ne kadai mafita domin ba'a san abin da zanga-zangar za ta haifar wa Najeriya ba idan tayi tasira har zuwa kwanaki goma ko fiye da haka.
Tsohon dan takaran shugaban kasan ya kuma gardadi masu niyyar zanga-zangar da suyi taka-tsan-tsan don kaucewa amfani da hanyar da ba ta dace ba wajen illata zababbiyar gwamnati.
Gbenga Hashim yace, duk da cewa yan kasa na da yancin gudanar da zanga-zanga kamar yadda tsarin mulkin kasa ya tanadar, akwai tsoron kada wasu su buya a bayan zanga-zangar su aikata abin da bai kamata ba.
Hashim yace, don haka, akwai bukatar gudanar da zanga-zanga cikin lumana kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya da ma dimukradiyya suka shimfida.